Daga Rahama Umar Kwaru
A yau Alhamis, 16 ga watan Febrairu, shahrarriyar yar dandalin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta sake gurfana gaban kotun shari’ar Musulunci dake Filin Hoki jihar Kano.
An kuma tisa keyyar Aminu Ibrahim da Sadiq Sharif Umar, da Ashiru Idris mai wushirya bisa zargin kalaman batsa a shafin Tiktok zuwa gidan yari mako 1.


Laifukan da ake tuhumar su ka iya bata tarbiyar yara masu tasowa, wanda su ka kuma saba da sashi na 355 da 356 da kuma 358 na kundin laifuffuka na kotun Shari’ar Musulunci.
Murja Ibrahim kunya ta musanta tuhumar da ake yi mata amma abokin burmunta Ashiru Idris mai wushirya ya amsa laifin sa.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa kotun ta aike da Murja Ibrahim Kunya gidan yari sakamakon wata kara da wasu Malamai a kano suka shigar kan rashin tarbiyya da Murja ta ke yi a shafukan sada zumunta.