Daga Halima Musa Sabaru
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Wudil da Garko Engr Muhammad Ali Wudil ya yi alkawarin cigaba da gudanar da aiyukan da zasu inganta tattalin arziki da rayuwar al’umma yankin da yake wakilta.
Engr. Muhammad Ali ya bayyana hakan ne yayi mika sabon inji transfomer ga al’ummar garin ‘yan sarki dake karamar hukumar Wudil.

Dan majalisar wanda mataimakin Shugaban karamar hukumar Wudil Hon. Labiru Isma’il ya wakilta, yace an samar da iniin transformer ne don magance matsalolin da al’ummar garin suka jima suna fama da ita, sakamakon tsufan da ta baya ta yi.

Yace transformer sabuwar ce fil aleda yana fatan zata magance matsalolin da al’ummar suka dade suna fuskanta, Inda yayi matan zasu bata kulawar data dace don gudun kada bata gari su lalata ko su saci wani abun daga jikinta.
Engr. Muhammad Ali Wudil ya kuma bukaci al’ummar garin dana kananan hukumomin Wudil da Garko dasu dubi irin aiyukan da jam’iyyar APC ta gudanar a yankin, su fito a ranar zabe don zabar dukkanin yan takarar da jam’iyyar ta tsayar don cigaba da yi musu aiyukan alkhairi.