Ganduje Ya Nada Yusuf Datti A Matsayin Babban Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomi

Date:

Daga Halima Musa Sabaru
 Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da tura Yusuf Datti Husaini ma’aikatar kananan hukumomi ta jiha a matsayin sabon babban sakatare na ma’aikatar.
Gabanin tura shi ma’aikatar, Sabon baban sakataren tsohon darakta albashi ne na ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jiha .
Talla
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
 Bayan rantsar da shi yau Alhamis a gidan gwamnati, gwamna Ganduje ya umarce shi da ya kasance a shirye a kodayaushe ya amince da ci gaban fasaha a aikin gwamnati tare da yarda da mafi kyawun aiki na duniya.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
  •  “ bayanai sun nuna kana da kwarewa kuma ka cancanci sabon matsayin da aka baka, muna sa ran ka ci gaba da yin kyakkyawan wannan tarihi da kake da shi a aikin gwamnati,” inji shi.
 Gwamna Ganduje ya umurci sabon babban sakataren ya yi aiki tukuru tare da yin aiki tare da dukkan ma’aikatansa a ma’aikatar don ganin an sami nasarar da ake fata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...