Daga Halima Musa Sabaru
Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya amince da tura Yusuf Datti Husaini ma’aikatar kananan hukumomi ta jiha a matsayin sabon babban sakatare na ma’aikatar.
Gabanin tura shi ma’aikatar, Sabon baban sakataren tsohon darakta albashi ne na ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta jiha .

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamna Malam Abba Anwar ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.
Bayan rantsar da shi yau Alhamis a gidan gwamnati, gwamna Ganduje ya umarce shi da ya kasance a shirye a kodayaushe ya amince da ci gaban fasaha a aikin gwamnati tare da yarda da mafi kyawun aiki na duniya.

- “ bayanai sun nuna kana da kwarewa kuma ka cancanci sabon matsayin da aka baka, muna sa ran ka ci gaba da yin kyakkyawan wannan tarihi da kake da shi a aikin gwamnati,” inji shi.
Gwamna Ganduje ya umurci sabon babban sakataren ya yi aiki tukuru tare da yin aiki tare da dukkan ma’aikatansa a ma’aikatar don ganin an sami nasarar da ake fata.