Daga Auwalu Alhassan Kademi
Dan channan da ake zargi da kashe Ummita Mr.Frank GengΒ yace ya fuskanci wulakanci da cin zarafi daban-daban daga marigayiyar Kuma ya ce ita ce ta dauko wuka Tayo kansa shi kuma ya murdeta ya kwace.
A zaman kotun na ranar Laraba karkashin jagorancin Mai Sharia Sanusi Ado Ma’aji Mr.Frank ya cigaba da bayyana yadda suka dinga mu’amala da ita.

Inda ya ce tun ranar da yataho gidansu ya yi mata waya saita Aiko Masa da sakon karta kwana inda ta fada masa kalmoman da basu kamata ba, Kuma bayan ya zo gidan ya shafe tsawan lokaci Yana buga Kofa suki bude Masa kofar Sai daga bisani makocinsu wato Mustapha ya bugawa kanwarta waya ya ce ta zo tabude Kuma ta karbi Karan mai suna Chali ta shiga dashi Kuma ta kulle Kofar.

Daganan ya ci gaba da bugawa har aka bude ya shiga cikin gidan harma ya bayyanawa kotu cewar abin da yakara bashi haushi yadda ruwan sama ya yi Masa Duka sunajinsa.
Ya ce bayan ya shiga Sai ta kama zaginsa harma ta zabga Masa Mari Sau hudu ya ce wannan Marin ba shi ne karon farko ba.
Β Daga karshe kuma ta shiga daki ta dauko wuka tana neman caka Masa shi kuma yakwace anan ne suka cigaba da kokawa.
Har Gilashin fuskansa ya fadi kasa wanda da shi ne yake taimaka masa wajen gani.
Lauyansa Barista Muhammad Balarabe Dan Azumi yaroki kotu da abasu wata ranar domin cigaba da Kare kansa kotun ta amince ta Sanya ranar 7 da 8 ga watan biyu na wannan shekarar.