Daga Kamal Yahaya Zakaria
Dan takarar gwamna na jam’iyyar adawa a Kano, NNPP Alhaji Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida) ya nemi a gurfanar da shugaban jam’iyyar APC na jihar Abdullahi Abbas a gaban kuliya.
Abba Kabir a kara mai lamba FHC/KN/CS/02/2023 wanda lauyansa Barr. Bashir Yusuf Muhammad Tudunwazirchi ya bukaci babbar kotun da ta gaggauta tilasta wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya binciki Abdullahi Abbas tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa furucinsa wanda zai iya haifar da rikicin siyasa a jihar Kano.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Abba Gida Gida ta bayyana cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP ya garzaya kotu da nufin zaburar da ‘yan sandan su yi abin da ya kamata.
- “Mun rubuta korafe-korafe da dama tare da kwararan hujjoji kan yawan ta’asar da shugaban jam’iyyar APC na jihar kano ya yi, amma har yanzu hukumar ‘yan sanda a Kano ba ta ɗauki wani mataki ba akan sa.” in ji Dawakin Tofa.

Umurnin idan har aka amince da shi, zai tilastawa rundunar ‘yan sandan Kano sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya dora mata, tare da yin aiki da irin wannan korafin da aka rubuta a kan shugaban jam’iyyar APC na jihar Abdullahi Abbas kan kalaman nuna kiyayya, cin zarafi da tunzura ‘yan bangar siyasa don tada rikici a jihar Kano .
A cewar Sanusi Bature Dawakin Tofa, za kuma a binciki Abdullahi Abbas kan zargin kisa da ya yi a wata ganawa da manema labarai.
- “Yayin da zaben 2023 ke kara karatowa, muna son mu taka rawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya ga daukacin al’ummar Kano da mazauna yankin wajen baiwa kowa yancin sa”.