Jin dumi: Kai garwashi daki ya yi sanadiyar mutuwar miji da mata a Kano

Date:

Daga Ibrahim Abubakar Diso

 A ranar Litinin da ta gabata ne aka tsinci gawar wani Sulaiman Idris mai shekaru 28 da matarsa ​​Maimuna Halliru mai shekaru 20 a kan gadon aurensu a Kano.
 Kadaura24 ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Larabar nan.
 SP Kiyawa ya ce an gano gawarwakin ne bayan da aka lura ba su fito daga gidan aurensu ba tun ranar 02/01/2023 da misalin karfe 11:00.
Talla
 Ya bayyana cewa “A ranar 03/01/2023 da misalin karfe 2100 na safe, sun sami rahoto daga garin Kwa, dake karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano cewa wasu ma’aurata, Sulaiman Idris, mai shekaru 28 da matarsa Maimuna Halliru, ’yan shekara 20 an fahimci cewa ba su fito daga gidan su ba tun ranar litinin 02/01/2023 da misalin karfe 2300.
 A binciken da aka gudanar, an gano cewa ma’auratan da suka rasu, sun kunna wuta don dumama dakinsu saboda sanyin da ake yi, inda suka kulle dakin, hakan tasa hayakin ya yi sanadiyar mutuwar su, Amma dai har ana kan gudanar da wani binciken.
Talla
 Lokacin da kakar mijin ta bude kofar dakin nasu, sai ta tarar da ma’auratan akan gadon su ba sa motsi, da wani warin hayaki a dakin.
Da samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mamman Dauda. ya umurci tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Ahmed Hamza, jami’in ‘yan sanda na shiyya (DPO), shiyya ta Dawakin Tofa da su wuce wurin. An kwashe mutanen da lamarin ya rutsa da su, aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano inda wani likita ya tabbatar da mutuwar ma’auratan.
 Kwamishinan ‘yan sandan ya shawarci al’ummar jihar Kano da su yi taka-tsan-tsan wajen amfani da wuta a wannan lokaci na hunturu, da wutar lantarki da kuma daukar matakan kariya .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...