Yan sandan Ghana sun gargaɗi shugabannin addinai game da al’adar hasashen abubuwan da za su faru a sabuwar shekara, wanda ke janyo fargaba da rikici har ma da mace-mace a ƙasar.
A wata sanarwa da ‘yan sandan ƙasar ta fitar ta ce bai kamata ‘yancin addini ya saɓa wa ‘yancin wasu ba.
Masu suka dai na ganin wannan sabuwar doka a matsayin wacce ta saɓa wa ‘yancin addini wanda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadar, dan haka dokar ba ta kan ƙa’ida.

Miliyoyin kiristoci ne dai ke taruwa a majami’u domin sauraron hasashen abubuwan da za su faru a shekara mai kamawa daga bakunan fastocinsu.
Sakonnin kan kunshi bushara kan abubuwa na farin ciki da garɗari kan munanan abubuwa.
‘Yan sandan sun sanya wannan doka ne bayan a shekarar da ta gabata aka yi hasashen samun yawan mace-mace da bala’o’i masu yawa a ƙasar.