Bai kamata a sami talauci a Arewacin Nigeria ba – Kashim Shattima

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Dan takarar mataimakin Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC Sanata Kashim Shattima yace Idan Akai la’akari da tarin arzikin kasa da ake da shi a Arewacin Nigeria bai kamata a sami talauci a yankin ba.

 

Sanata Kashim Shattima ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci gidan tsohon gwamnan jihar Kaduna zamanin mulkin soja Gen. Lawan Jafaru Isa Mai ritaya .

 

Talla
  • ” Mun je jihar jigawa jiya mun ga arzikin kasa haka a nan kano ma, ta yadda ko takardar kudi aka shuka sai ta tsiro saboda yadda Allah ya albarkaci mu da albarkar kasa da kuma yawan jama’a , don haka babu dalilin da za’a Sami talauci a Arewacin Nigeria”. Inji Shattima

 

Yace akwai yiwuwar nan da shekara ta 2050 Nigeria zata zama ta uku cikin jerin kasashen da suka fi yawan al’umma a duniya Inda zai zama daga Chana sai Indian sai Kuma Nigeria.

 

Kashim Shattima ya kara da cewa a shekara ta 2050 arewacin Nigeria zai kasance da kaso 70 na yawan al’ummar Nigeria, don haka ya bukaci shugabannin arewa su gada kai don samarwa yankin makoma Mai kyau.

 

A shirye muke mu taimaka don inganta aiyukan yan Hisbah a Kaduna – Kwamandan Hisbah na Kano

Ya yi alkawarin idan suka lashe zaben 2023, gwamnatin su zata bujiro da hanyoyin da zasu samar wa matasa aiyukan yi don inganta Rayuwar su da tattalin arzikin kasa.

 

Da yake nasa jawabin Gen. Lawan Jafaru Isa ya bada tabbacin zai cigaba da yin duk mai yiyuwa wajen ganin jam’iyyar APC ta yi nasara a dukkanin zabukan dake tafe ta karkashin kungiyar sa .

Kashim Shattima ya kuma ziyarci Alhaji Musa Gwadabe wanda ya je ya duba shi tare da neman tabarrakinsa a takarar da suke yi kasancewar sa cikin iyayen jam’iyyar APC na kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...