Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi zargin cewa ana yunkurin yi masa magudi a zaben gwamnan da za a gudanar a 2023.
Ya bayyana haka ne ranar Lahadi a gidan gwamnatin jihar Bauchi yayin da kungiyar Kiristoci ta jihar ta kai masa ziyarar bikin Kirsimeti.

Gidan talbijin na Channels TV ya ambato Gwamna Bala Mohammed yana cewa mutanen da suke yunkurin yin amfani da karfin gwamnatin tarayya domin yin magudin zabe ba za su yi nasara ba domin Shugaba Muhammadu Buhari ba zai bari hakarsu ta cimma ruwa ba.
“Akwai mutanen da ke sayen kuri’u, da kuma wadanda suke shirin murde zabe ta hanyar amfani da karfin gwamnatin tarayya amma na sani cewa Shugaba Buhari mutum ne mai adalci, kuma tuni ya tabbatar mana cewa zai bar mutane su zabi wanda suke so,” in ji shi.