Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce masu son tayar da fitina a ƙasar “sun gaza yin hakan”, yana mai cewa “alkairi na tafe a 2023 da gabanta” cikin jawabin Kirsimetinsa na ƙarshe a matsayin shugaban ƙasa.
Cikin jawabin da ya gabatar a ranar Asabar, Buhari ya jaddada cewa nan da watan Mayu gwamnatinsa za ta miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin da za a zaɓa a babban zaɓe na watan Fabarairu.

“Saƙona kenan na Ranar Kirsimeti a matsayin shugaban ƙasa,” in ji shi. “Nan da mako 22 daga yanzu wannan gwamnatin za ta miƙa mulki ga wata.”
Kazalika, ya bayyana miƙa mulkin a matsayin “dama ta tabbatar da kafuwar dimokuraɗiyya a Najeriya kamar yadda ƙasashen waje suka sani”.
A cewarsa: “Mu ci gaba da zama lafiya cikin annashuwa har zuwa sabuwar shekara da kuma lokacin zaɓe a watan Fabarairu da ma gaba.
“Ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa waɗanda ke neman tayar da fitina a ƙasarmu sun gaza a yunƙurinsu.”