Yanzu-Yanzu: Shekarau ya Magantu kan hukuncin kotun da ya tabbatar da Muhd Abacha a takarar gwamnan kano na PDP

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Ibrahim Shekarau, ya ce suna jiran umarnin da uwar jam’iyyarsu ta ƙasa za ta bayar bayan kotu ta bai wa Mohammed Abacha takarar gwamnan Kanon.

Shekarau ya faɗa wa BBC Hausa cewa “burinmu shi ne ‘yan jam’iyya su natsu, ɓangaren da ya yi nasara da wanda bai yi ba su kwantar da hankalinsu har sai an samu umarni daga jam’iyya”.

A ranar Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tabbatar da Mohammed Abacha a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamna a PDP tare da soke zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa Sadiq Aminu Wali nasara.

Talla

Hakan na nufin ɓangaren shugabancin Shehu Wada Sagagi ne ya yi nasara, wanda ya shirya zaɓen, saɓanin ɓangaren Sanata Bello Hayatu Gwarzo da ke mara wa Sadik Wali baya.

Shekarau ya shiga PDP a watan Augusta bayan rashin jituwa tsakaninsa da jagora kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...