Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun 26 da 27 ga watan Disamba da kuma 2 ga watan Janairun 2023 a matsayin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Ministan cikin gida Alhaji Rauf Aregbesola ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar Belgore Shuaib a ranar Juma’a.

Sanarwar ta kara da cewa, bukukuwan su ne na bikin Kirsimeti, da washegarin ranar, da bikin Sabuwar Shekara .
Aregbesola ya umurci Kiristoci da su yi koyi da Yesu kuma su yi tunani a kan koyarwarsa yayin da suke bikin.
Ya kuma yi kira ga mabiya addinin kirista da kada su bari masu ra’ayin aikata laifuka su ingiza su su haifar da rikici a kasar.