Rikicin PDP a Kano: Tutar da aka ce wai an baiwa wasu yan takarar PDP a kano rashin girmama doka ne – Sagagi

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Kano Alh. Shehu Wada Sagaga ya nesanta kansa da sauran Shugabannin jam’iyyar na jiha daga gabatar da tutoci ga β€˜yan takarar jam’iyyar a jihar.

 

A martanin da shugaban ya sanya wa hannu da kansa tare da aikowa kadaura24 a Kano, shugaban ya bayyana taron a matsayin wani bangare na yaudarar yan jam’iyyar gabanin zaben 2023.

 

Shehu Sagagi ya kara da cewa duk wasu al’amura da suka shafi ya Allah takarar jam’iyyar PDP a kano zasu cigaba ne bayan hukuncin kotu da ake sa rai yau Litinin 19 ga watan Disamba 2022.

Talla

β€œA halin yanzu ba za mu iya ba wa kowa daga cikin β€˜yan takarar gwamnan kano su biyu tuta ba, domin suna gaban kotu suna jiran hukunci, a matsayinmu na β€˜yan kasa masu bin doka da oda, dole ne mu jira sakamakon hukuncin kotun da ke tafe nan gaba kadan kafin mu yi wani abu daya shafi yan takara”.

 

Sagagi ya kuma tabbatar wa da β€˜yan jam’iyyar PDP na Kano cewa ba da tutoci da aka yi a ranar Asabar an yi shi ne ba tare da amincewar Shugabannin jam’iyyar na jiha ba, don haka jama’a su yi watsi da taron domin ba komai ba ne illa nuna rashin mutuntawa ga doka da oda ta yadda zai haifar da rarrabuwar kawuna da rage damar cin zabe ga jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

 

β€œIna so in tabbatar wa kowa da kowa cewa za mu sanar da rana da lokacin da za a mika tutar jam’iyyar a hukumance ga duk β€˜yan takarar jam’iyyar PDP bayan hukuncin kotu Insha Allahu “.

 

Ya kuma yi kira ga daukacin β€˜ya’yan jam’iyyar PDP da magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Kano da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda tare da yin watsi da duk wasu bayanan da ba su fito daga jam’iyyar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related