Daga Abdulhamid Isah D/Z
Shugaban kungiyar daliban Jami’ar Yusuf maitama sule dake kano Kwamaret Muhammad Inuwa Imam ya bukaci dan takarar gwamnan jihar kano na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da yafi mayar da hankalin wajen bunkasa ilimin matasa domin shi ne kashin bayan duk wani mutum, idan ya zama gwamnan kano.
Kwamaret Muhammad Inuwa Imam ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da wakilin Kadaura24 a kano.
Yace Ilimi shi ne yake kai kowacce irin al’umma ga managarciyar rayuwa domin shi ne zai baiwa Shugaban damar yanke Hukunci ba bisa jahilci ba, wanda hakan zai inganta rayuwar al’ummar da ake mulka.

” Matukar dai mai grima gawuna ya bunkasa rayuwar matasa da Ilimi to ko shakka babu kome zai zomasa acikin sauki, domin kasashen da suka cigaba sun samu hakanne ta fannin bunkasa rayuwar matasansu da kasuwancinsu hakan tasa suka buwaya a duniya”. Inji Muhd Imam
Shugaban Daliban ya kara da cewa suna goyon bayan takarar gwamnan Kano da Dr. Nasiru Yusuf Gawuna yake yi a jam’iyyar APC, saboda irin gudunmawar da ya baiwa ilimi tun lokacin da yake Shugaban karamar hukumar Nasarawa, do haka muke da yaƙinin idan Allah ya tabbatar da Gawuna a gwamna zai yi kokarin gina rayuwar matsa a fadin wananan jiha ta Kano .
Kwamaret Muhammad Inuwa Imam ya kara da cewa yawancin sauran gwamnatoci suna mai da hankali ne wajen gina matasa a bangar siyasa wanda hakan zan lalata rayuwar matasan, Inda ya kara da cewa bunkasa ilimin matasa to koshakka babu kan bunkasa kasuwancin su domin yawancin yan kasuwa matasa ne.