Daga Abdulbaki Ali Ahmad Sharifai
Babbar kotun shari’ar musulnci dake filin hoki karkashin jagorancin mallam Abdullahi Halluru Abubakar, ta ci gaba da sauraron shari’ar nan da ake yi tsakanin Iyalan tsohon Kwamishinan shari’a na jihar Kano marigayi Barrister Aliyu Umar SAN da Dr Nasiru Adamu Aliyu mai lambar SAN, kan takaddamar mallakar kamfanin lauyoyi na AA ALIYU &CO.
A zaman kotun lauyan da yake kare wanda ake zargin ya bayyana cewa yaune ranar da kotun ta sanya domin gabatar da takardar da take nuna cewa wanda ake karar yana da hadaka da kamfanin marigayin da ake takaddamar akansa.

Sai dai ya bayyanawa kotun cewa sunyi duk iyakar kokarinsu akan neman takardar daga hukumar kula da rajistar guraren kasuwanci ta kasa CAC reshen jihar Kano, sunce tuni suka daina bada kwafin takardar mallakar sai dai har sun samu umarni daga kotu.
A zaman daya gudana lauyan ya ya mika rokonsa ga alkalin da ya bada takardar umarni ga hukumar don samun kwafin takardar, sai dai da alkalin ya waiwayi lauyan dake kare wadanda suke korafin barrister Bashir Muhammad kan rokon lauyan baiyi suka ba.
Daga nan ne Alkalin ya karbi rokon ya kuma yi umarni da a rubuta takarda ga hukumar ta CAC data bada kwafin takardar ya kuma dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 24/12/2022 domin cigaba da shari’ar.
bayan fitowa daga kotun wakilin mu ya yi kokarin jin tabakin lauyoyin kawane bangare amma sunki cewa uffan.