Tsadar Man fetur ta jawo kayan masarufi sun tashi, ya kamata gwamnatin kano ta shiga lamarin

Date:

Daga: Ibrahim Sani Gama
Kungiyar yan kasuwa ta karamar hukumar kabo ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta zauna da dillalan man fetur da sauran masu ruwa da tsaki a fannin man domin kawo dai-daiton da zai kawo karshen wahalar man da ake fama da shi a jihohin kasar nan.
Gura cikin jagororin kungiyar Alhaji Mamuda zangon-kabo ne ya yi kiran lokacin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 a Kano.
Zangon-kabo kabo ya ce zama da yan kasuwar da suke shigo da man yana da mutukar mahimmanci domin jin makasudu da yasa man yake wahalar samu da kuma tsada a wasu daga cikin gidajen man fetur.
Talla
Ya ce kamata yayi gwamnati ta dauki mataki kasancewar matsalar ta shafi fannoni da dama ciki har da kasuwanci saboda farashin kayayyakin masarufi ya tashi a kasuwanni da kudaden ababen hawa, wanda ya jayo talakawa suke fuskantar kalubale da yawa.
Ya ce zaman shine abin da zai kawo kyakyawar fahinta a tsakanin dukkan bangarorin da abin ya shafa da nufin samarwa alumma sauki a harkokin rayuwarsu ta yau da kullum.
Haka zalika, ya shawarci alumma kasar nan da su kasance masu gudanar da addu’oin samun sauki akan al’amura da suke damun su musamman matsalolin rashin tsaro daya zama ruwan dare gama duniya.
Mamuda Zangon-kabo ce gwamnati tana da rawar takawa a fannoni da yawa kasancewar itace uwar kowa wadda take da hanyoyin da za ta samarwa alumma abubuwan more rayuwa da sauran kayayyaki da zai iya amfana.
Ya ce akwai bukatar alumma su rika yiwa su shugabannin su addu’oi domin basu kwarin gwiwar aiwatar ayyukan ci gaba mai dorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...