Gwamnatin jihar kano ta bukaci gwamnatin tarayya data bincika tare da hukunta shugabannin kula da aikin hajji ta kasa Nahcon sakamakon gazawarsu wajen shirya aikin hajji bana yadda ya kamata.
Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan lokacin da yake karbar rahoton aikin hajjin bana daga hukumar Jin dadin alhazai ta jihar kano.

Gwamna Ganduje yace tun da ya zama gwamnan kano bai taba ganin yadda hukumar tayi Rashin tsari ba kamar shekarar data wuce, Inda yace akwai rashin gaskiya da kwarewa a aiyukan shugabannin hukumar Nahcon na wannan karo.
” Sun cuci alhazai su cuci ma’aikata, sun kawo chanje-chanje marasa ma’ana, sun kawo Rashin gaskiya da son rai sun kasa kai alhazai Kuma sun cucesu”. Inji Ganduje
” Sun bamu jirgin da zai yi jigilar alhazan mu, mun fada musu bama so, ni da katina ma sai da naje har ofishin hukumar dake abuja na Kuma koka musu suka ce min zasu gyara, Amma bayan tahowa ta suka ki chanzawa”.
Ganduje ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da majalisar wakilai ta kasa da su bincika domin daukar matakan da suka dace don hana faruwar hakan a nan gaba.
Ya kuma yabawa hukumar Jin dadin alhazai ta jihar kano bisa yadda suka gudanar da kyakyawan tsari a aikin hajjin daya gaba.