Adaidaita sahu: Gwamnatin Kano ta yi wasa da hankalin al’ummar Kano – Sha’aban Sharada

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 Dan takarar gwamna na jam’iyyar ADP, kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar birni, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada OON, ya yabawa al’ummar kano bisa yadda suka nuna dattako kan dokar hana yan adaidaita sahu bin wasu manyan tituna a kano, da gwamnatin jihar kano ta yi a ranar Laraba, 30 ga Nuwamba, 2022.
 A wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan kano, Abbas Yushau Yusuf ya fitar, dan takarar gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan janye dokar da gwamnatin jihar ta yi cikin kasa da sa’o’i 24 bayan aiwatar da dokar.
 Sha’aban Ibrahim Sharada ya ce jama’a sun nuna wa gwamnatin jiha ta hanyar dimokuradiyya cewar basu shirya karbar dokar ba saboda zata musguna musu ta fannoni daban-daban musamman ta fuskar tattalin arzikin al’ummar Kano.
Talla
 Ya ce lamarin ya nuna wa ‘yan Najeriya da kasashen duniya cewa, al’ummar Kano sun shirya tsaf domin kawo sauyi a zaben gwamnan da za a yi a ranar 11 ga Maris, 2023, wanda jam’iyyar ADP ce za ta cinye zaben.
 Sharada ya ce al’ummar Kano shaida ne kan yadda kwamitin yakin neman zaben sa suka nuna damuwarsu kan matsanancin halin da al’ummar jihar kano suka shiga a ranar laraba sakamakon dokar hana yan adaidaita sahu bin wasu manyan tituna kano.
 Dan takarar ya kalubalanci Mataimakin Gwamnan Kano, inda ya ce, “Wane ne dan takarar Gwamna na APC da zai gaya wa jama’a cewa Mai gidan sa yayi kuskure ? A ina suka sami kuskuren me yasa ba ayi kyakyawan tsari ba Kuma me yasa ba’a gudanar da kyakyawar tuntuba kafin aiwatar da dokar ?
 Ya kuma bukaci masu rike da mukaman Kano guda biyu da su gaya wa al’ummar Kano dalilin da ya sa aka dauki matakin ba tare da tuntubar ba duk da sanin wahalhalun da mutane za su shiga a sakamakon ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ku ba da gudunmawa kano ta zauna Lafiya – Waiya ya shawarci yan jaridun yanar gizo

Gwamnatin jihar Kano ta bukaci kafafen yada labarai na...

KAROTA ta tabbatar da aniyarta na inganta matsayin jami’anta

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano...

Sarkin Sanusi ya amince da nadin sabon mai unguwar Hotoro GRA

  Mai martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi...