Daga Rukayya Abdullahi Maida
A fadin Najeriya gaba daya, Jihar Sokoto ce tafi yawan Talakawa, bisa jadawalin TheCableIndex.
Gwamnatin Buhari dai a bayan ta yi alkawarin fitar da yan Najeriya milyan 100 daga cikin kangin talauci.
Ga jerin adadin mutanen da cikin talauci a jihohin Arewa maso gabas:
Sharhi
Bisa jadawalin, mutum kashi 9.5% na al’ummar jihar Sokoto ne kadai suke ci su koshi lafiya kulli yaumin.

Jihar Jigawa da Kebbikuwa, kashi 15% kacal ke samun cin abincin N500 da safe, N500 da rana, kuma N500 da dare. A jihar Kaduna da Zamfara, kashi 26% dan dauri ne masu walwala.
Yan jihar Kano ne kadai suke da masu walwala da ya haura kashi 30%. Duk da haka, mutum biyu cikin ukun yan jihar Kano basu ci su koshi yadda ya kamata a rana.
Wannan Alkaluma na nuna cewa mafi akasarin al’ummar yankin Arewa maso yamma Talakawa ne.
Wadanda talauci yafi afkawa sune masu iyalai da yawa saboda zasu ji da kudin abinci, kudin muhalli, kudin makaranta da kudin kiwon lafiyan iyali.