Daga Idris Auwal Malumfashi
Gwamna Masari ya fashe da kuka yayin da yake gabatar da kasafin kudin sa na karshe ga majalisar dokokin jihar Katsina.
Katsina Post ta samu cewa Gwamnan ya bayyana a gaban majalisar ne tare da rakiyar mataimakin sa da sauran mukarraban gwamnati ranar Talata domin gabatar da kundin kasafin kudin na shekarar 2023.

Kasafin kudin na shekarar 2023 dai ya kai sama da Naira Biliyan 288.
Wannan dai shi ne kasafin kudin na karshe da Gwamnan ya kai majalisa kamar yadda Kundin tsarin mulki ya tsara , domin zai kammala wa’adin mulkin sa ne a watan Mayu na shekarar 2023 mai zuwa.
Cikin jawabin sa a zauren majalisar, Gwamna Masari ya yabawa majalisar da bangaren Shari’a da ma Sarakunan gargajiya bisa irin hadin kan da suke ba gwamnatin sa tare da rokon su ci gaba da baiwa gwamnatin da zata gaje shi irin sa