Daga Maryam Abubakar Tukur
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu ‘yan uwa guda uku sakamakon wata gobara da ta tashi a Kabuga Yan Azara da ke karamar hukumar Gwale.
Da yake bayyana lamarin, jami’in hulda da jama’a na hukumar, PFS Saminu Yusif Abdullahi ya bayyana cewa gobarar da ta hada da wani bene ta faru ne a daren ranar Litinin.

Ya kara da cewa, gobarar ta tashi daga saman ginin ta yi sanadiyyar mutuwar wasu ‘yan uwa uku Saddiqa Salisu ‘yar shekara 6, Abdulsamad mai shekaru 15 da kuma ‘yar uwarsu Fatima Isiyaku.
Saminu Yusif ya yi nuni da cewa, gobarar ta laso wasu sassan ginin, sakamakon kasa sanar da hukumar kashe gobara ta jihar Kano a kan lokaci.
Ya kuma bukaci jama’a da su rika kula sosai tare da sanar da hukumar akan lokaci domin rage yawan asarar da za’a yi .