Daga Auwal Alhassan Kademi
Dan takarar gwamnan jihar Kano, a ƙarƙashin jam’iyyar ADP Sha’aban Ibrahim Sharaɗa, ya bada tabbacin sanya dokar ta baci a bangaren ilimi, a kokarin sa na ceto fannin jihar idan ya zama gwamnan jihar kano.
Sha’aban Sharaɗa ya bayyana hakan ne cikin wani jawabi da ya gabatar a yayin wani taron jin ƙudirin ƴan takar gwamna jihar Kano, a kakar zaɓe mai zuwa taron da Gidauniyar Dakta Aminu Magashi haɗin gwiwa da ƙungiyoyin farare hula na jihar su ka shirya.
Taron ya maida hankali kan batun yadda masu neman takarar gwamnan Kano za su inganta ɓangaren kiwon Lafiya da ilimi da , tsaro da kuma bunƙasa masana’antu da, samar idan su ka samu nasara.

Kazalika ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen yin duba na tsanaki kan dokokin ilimi matuƙar ya samu nasara.
Haka kuma ɗan takarar gwamnan ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci sallamar malamai ba sai dai za a duba inda ya dace a sanya su.
A karshe Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya kuma bayyana cewa yana da tanadi na musamman kan ilimi a jihar Kano da kuma samar da kayayyakin yanayin koyo da koyarwa har ma da inganta manyan makarantun gaba da Sakandire.