Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Wani jigon jam’iyyar PDP a Kano, Jafar Sani Bello, ya shawarci Mohammad Sadiq Wali da ya bar kotu ta yanke hukuncin waye dan takarar gwamnan Kano na PDP a 2023.
Kwanan nan Sadiq Wali ya ce zaben fidda gwani da ya samar da Mohammaf Sani Abacha ba ingantacce ba ne.
A halin yanzu dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC Sadiq Wali ta amince da shi a matsayin dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP.

Kwanan nan ya bayyana cewa zaben fidda gwanin da ya samar da shi a matsayin dan takarar PDP halastacce ne, yayin da wanda ya samar da Muhd Abacha a matsayin maras inganci.
Da yake zantawa da Majiyar Kadaura24 a ranar Juma’a, Jafar Sani Bello, guda cikin wadanda suka nemi takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP, ya shaida wa Sadiq Wali cewa ya jira sakamakon shari’ar dake gaban kotu wadda za’a yanke a ranar 25 ga watan Nuwamba.
“Ina nan Ina ci gaba da kalubalantar cancantar Mohammed Abacha da Sadiq wali a gaban kotu bisa doron kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, da dokar zabe da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP” . Inji Jafar
“Wannan shari’a tana gaban wata babbar kotun tarayya da ke Kano, kuma mai shari’a A. M Liman ne ke jagoranta. Maganar da Sadiq Wali ya yi da yan jaridu rashin mutuntawa ne da girmama kotu.
Jafar Sani Bello ya kara da cewa “Ya kamata ya fahimci cewa idan al’amuri yana gaban kotu, ba’a magana da yan jaridu akan sa sai bayan anyi hukunci na karshe akan batun, Kuma za’a yi hukunci a kan wannan lamari a ranar 25 ga Nuwamba, 2022,” in ji Jafar Bello.