Abubuwa 3 da Musa Iliyasu Kwankwaso yafi sauran yan Siyasa da su

Date:

Ra’ayin Musa Dan Zaria

Musa Iliyasu Kwankwaso ya rike mukamin a daban-daban kama daga matakin jam’iyya da Kuma na mulki a lokuta mabanbanta.
Wadannan mukai da Musa Iliyasu Kwankwaso ya rike a Kano su ne suka bashi damar samun wasu abubuwa guda 3 da ya kamata a ce sauran yan siyasa suna da su don su amfani kansu da kuma al’umma.
Ga abubuwa 3 da Musa Iliyasu Kwankwaso ya yiwa sauran yan siyasa zarra da su :
MU’AMALA: Babu shakka duk wanda yasan Musa Iliyasu Kwankwaso ko ya taba mu’amala da shi, dole ne zai yi masa shaidar kyakyawar mu’amala da mutane ba tare da la’akari da matsayin mutum ba.
Daga cikin kyawawan halayyar Musa Iliyasu Kwankwaso yana amfa gayyata idan an gayyace shi suna daurin aure da duk wata sabga ta arziki, akan wannan al’ummar madobi shaida ne domin su suke zaune da shi a kodaushe tun tasowarsa har Allah ya kai shi matsayin da yake yanzu.
Musa Iliyasu Kwankwaso yana zuwa duba marasa lafiya da kuma gaisuwar mutuwa a duk Inda ya sami labari, a ko Ina Kuma idan ya haka yake tasowa ba, sai ya ajiye Wani abun hasafi don taimakawa wadanda abun ya shafa.
TAIMAKAWA AL’UMMA: Babu shakka taimakawa al’umma guda ne cikin kyawawan dabi’un Musa Iliyasu Kwankwaso hannan ma tasa ake yi masa lakabi da “Musa kowa ya bika bai bi Kaho ba”.
Akan Wannan batu kowa shaida ne kan yadda mutane da yawa sukai arziki da Musa lokacin yana kwamishinan yara karkara na farko dana biyu dana uku, shi kansa bana Jin yasan adadin mutane da ya fitar daga cikin mawuyacin hali tunda gada wancan lokaci har yanzu.
Ya kai Mutane makka, ya Siyawa da yawa gidaje ya bada motocin da buburan da shi kansa bai San adadin su ba, sannan Musa Iliyasu Kwankwaso ne kadai dan Siyasar da idan ka kai masa bukata zai yi maka abun da zai iya ba tare da yaudara ba.
TSAYAWA AKAN GASKIYA : Shi ma Wannan wani babban sha’ani ne da ake bukata shugabannin al’umma su kasance suna da shi, domin rashin tsayawa akan gaskiya ba karamin naka su ba ne akan Shugaba.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya sami shaidar yana tsayawa akan duk wani abu na gaskiya da ya shafi al’umma, Kuma koda mu’amala kuke da shi idan ya fahimci mutum bashi da gaskiya to hakan ya kan sa a sami matsala da shi.
Kuma kowa ya yarda tsayawa akan gaskiya shi ne ajiye komai a gurbinsa hakan Kuma shi ne adalci, shi Kuma adalci shi ne yake kawo Zaman lafiya a ko’ina a fadin duniya, to Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi fice akan hakan.
Wannan ce tasa mutane da yawa suke yiwa al’ummar yankin kura madobi da garun Mallam sambarka tare da Addu’ar Allah ya basu Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin dan majalisarsu na tarayya, domin su amfana fiye da kowanne lokaci a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...