Daga Rahama Umar Kwaru
Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero CFR ya yabawa Gwamnatin Dr. Abdullahi umar Ganduje bisa kulawar da take baiwa Ilimin addinin Musulunci da na Zamani a jihar.
Mai martaba Sarkin ya yi wannan yabon ne a wajen bikin yaye dalibai tamanin da daya na makarantar Ulumul quar,an li imamu Dalhatu, Islamiyya Soron Danki a karamar hukumar birni.
Alh. Aminu Ado Bayero, ya taya daliban murna tare da bukatar su da su yi amfani da ilimin da suka samu tare da yaba wa kokarin malaman makarantar wajen inganta tarbiyyar daliban.
Sarkin wanda ya yi jawabi mai tsaho kan muhimmancin Ilimi, ya kuma bayyana ilimin kur’ani a matsayin ginshikin duk wani ilimi a rayuwar dan Adam.

Cikin sanarwar da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa kadaura24, yace Alhaji Aminu Bayero, ya yi kira ga Masu dukiyoyi a cikin al’umma da su rika tallafa wa karatun kur’ani a tsakanin daliban da suka kammala karatu domin bunkasa ilimin kur’anin da suka samu.
Da yake jawabi a wajen taron shugaban makarantar Malam Habibu Abbas ya bayana tarihin makarantar da cewa an kafa makarantar tun shekarar 2010 da dalibai ashirin da takwas, kuma a yanzu haka tana da dalibai sama da dari da hamsin da shida da malamai da dama.
A nata bangaren, Malama Tasalla Nabulusi Bako, ta shawarci jama’a da su rika cika alkawuran da suka dauka a kowane lokaci, ta kuma yaba wa mai martaba Sarkin Musulmi Aminu Bayero bisa kulawar da yake baiwa cigaban Ilimi don bunkasa shi