Da dumi-dumi: Buhari ya amince da karin albashi ga alkalai

Date:

Daga Aliyu Nasir Zangon Aya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kuma bada umarnin a dauki matakan gaggawa wajen aiwatar da shirin inganta albashi da jin dadin ma’aikatan shari’a.
 Shugaban  Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, a wajen bikin kaddamar da Nabo Graham-Douglass Campus na makarantar koyon aikin shari’a ta Najeriya da ke Fatakwal ga majalisar ilimin shari’a.
Talla
 Babban Lauyan kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN ne ya wakilci Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taron.
 Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Dr. Umar J|ibrilu Gwandu, mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, a ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a.
 A cewar sanarwar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci shugaban hukumar tattara kudaden shiga da ta rabon arzikin kasa da babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a da su gaggauta fara daukar matakan tabbatar da aiwatar da shirin inganta albashi da walwala ga jami’an shari’a. kasa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sake maka Ganduje da ya’yansa a gaban Kotu

Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr....

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...