Daga Aliyu Nasir Zangon Aya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kuma bada umarnin a dauki matakan gaggawa wajen aiwatar da shirin inganta albashi da jin dadin ma’aikatan shari’a.
Shugaban Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, a wajen bikin kaddamar da Nabo Graham-Douglass Campus na makarantar koyon aikin shari’a ta Najeriya da ke Fatakwal ga majalisar ilimin shari’a.

Babban Lauyan kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN ne ya wakilci Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen taron.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Dr. Umar J|ibrilu Gwandu, mataimakin na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, a ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a.
A cewar sanarwar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci shugaban hukumar tattara kudaden shiga da ta rabon arzikin kasa da babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a da su gaggauta fara daukar matakan tabbatar da aiwatar da shirin inganta albashi da walwala ga jami’an shari’a. kasa