Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shahararren malamin addinin musuluncin nan wanda ya shahara wajen karanta al-qur’ani Mai girma a kano da kasa baki daya, Alaramma Ahmad Sulaiman ya ce masu ganin laifinsa don ya yiwa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu addu’a a wajen yakin neman zaben da aka yi a Jos kawai mahassada ne da kuma wadanda basu fahimci yadda rayuwa take ba.
“ Shigar da muke yi harkokin siyasa ta taimaka wajen cigaban addinin Musulunci a arewacin Nijeriya dama kuma mun shiga siyasar ne don kare kimar addinin Musulunci” inji Alaramma Ahmad Suleiman

Alaramma Ahmad Sulaiman ya bayyana hakan ne cikin wata hira ta musamman da sukai da shafin DCL Hausa a ranar Juma’ar nan.
” Banga abun da yasa mutane suke damuwa ba saboda da na yiwa Tinubu addu’a, idan aka lura a baya na yiwa Kwankwaso na yiwa Ganduje da Sule lamido, sannan kuma na yiwa Atiku Abubakar, Amma duk ba wanda ake zance akan sa sai na Tinubu na rasa me yasa”. A cewar Ahmad Sulaiman
Yace al’umma da dama basu fahimci dalilin su na shiga Siyasa ba, Inda shi dai ya shiga siyasa ne don ya kare Martabar addinin musulunci kuma kundin tsarin mulkin kasa ya baiwa Malaman addinin musulunci damar shiga siyasa kamar kowa .

” Allah yace Malamai su ne managarta a Cikin al’umma to so kuke mutanen kirki su ki shiga Siyasa Saboda mutanen daba na kwarai ba su shiga don su sami dama su cutar da al’umma, ba yau na fara Siyasa ba kuma bazan daina ba”. Inji malamin
Daga ƙarshe yace ya rasa dalilin da yasa mutane suka damu dan ya yiwa Bola Tinubu addu’a, shi na gamsu zai taimaki Musulunci shi yasa nake binsa yakin neman zabe Kuma ma Ina da mukami da kwamitin yakin neman zaben sa”.