Al’ummar Mexico na jimamin mutuwar wata karya – wadda ta zama fitacciya wajen aikin ceton mutanen da girgizar ƙasar 2017 ya rutsa da su.

Rundunar sojin ruwan ƙasar ta ce karyar ta mutu ne sakamakon tsufa da ta yi.
Sanye da tubarau da takalman sau-ciki, karyar mai suna Frida ta yi aiki tuƙuru wajen kuɓutar da mutanen da gini ya rufta kansu a birnin Puebla a shekarar 2017.
A lokacin da take aiki da rundunar sojin ruwan ƙasar an kai Frida aikin ceto a ƙasashen Haiti da Ecuador.
A wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin ruwan ƙasar ta yaba da kyawawan halaye da biyayyar da karyar ta nuna a lokacin aikinta.