Daga Auwal Alhasan kademi
Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta kawo karshen taronta na kwamitin zartarwa na kasa (NEC) ta yanke shawarar baza sake shiga wani yajin aiki.
Sai dai kungiyar ta yi Allah-wadai da yunkurin gwamnatin tarayya na mayar da malaman jami’o’i kamar ma’aikatan wucin gadi ta hanyar biyansu Rabin albashin su.

A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata bayan kammala taron NEC, shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana cewa malaman jami’o’in cikakakkun ma’aikata ne ba na wucin gadi ba.
Ya ce kungiyar ta dakatar da yajin aikin na watanni takwas a ranar 14 ga Oktoba, 2022 bisa bin umarnin kotun ma’aikata ta kasa da kuma la’akari da kokarin tsoma bakin ‘yan Najeriya masu kishin kasa, ciki har da Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.
Osodeke ya kara da cewa matakin da kungiyar ta dauka alamu ne da suka nuna tsantsar biyayyar ta ga bangaren shari’a, da sauran cibiyoyi da ma’aikatun gwamnati a kodayaushe da suke kira ga kungiyar data sanya kishin kasa fiye da bukatun kansu .