Tinubu ya amince a sanya yan kannywood a kwamitin yakin neman zabensa

Date:

 

Darakta-Janar na yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Gwamna Simon Lalong, ya amince da shigar da ‘yan Kannywood cikin kwamitin.

 

Lalong, wanda kuma shi ne gwamnan Plateau, ya sanar da amincewar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dr Makut Maham, ya fitar a yau Talata a Jos.

Talla

Ya ce shigar da su wani bangare ne na kokarin zurfafa shigar da masu fasaha daga shiyyar Arewa a yakin neman zaben.

 

Babban daraktan ya ce amincewar ta biyo bayan ziyarar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Bola Tinubu ya kai Kano, inda ya gana da ‘ya’yan kungiyar.

 

Ya ce, Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa an baiwa ‘yan Kannywood damar shiga cikin yakin neman zabe domin baje kolin basirarsu, tare da taimakawa jam’iyyar ta samu nasara a zabukan dake tafe.

 

Lalong ya dora wa kungiyar alhakin hada kai tare da fadakar da dimbin mabiyansu a kan tallan Tinubu da kuma manufofinsa domin yi masa ruwan ƙuri’u a ranar zaɓe.

 

Sanarwar ta ce, kungiyar ta Kannywood ta na da Abdul-Mahmud Amart a matsayin Darakta, Ismail Afakallah a matsayin mataimakin darakta da Sani Mu’azu a matsayin sakatare, tare da sauran shugabannin da ke jagorantar bangarori daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...