Rikici tsakanina da Murtala Sule Garo ya kare – Alhassan Ado Doguwa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta kasa kuma dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa Hon. Alhassan Ado Doguwa yace ya yafewa Murtala Sule Garo duk abun da ya yi masa, kuma shi ma yace ya yafe masa.
” Gwamna Ganduje ya kirawo ni da shi Murtala da Nasiru Aliko koki da kuma shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Abbas, ya ji ta bakina ya ji ta bakin Murtala, ya kuma fadamin inda na yi kuskure shi ma kuma Murtalan an fada masa nasa laifin”. Inji Doguwa
Hon. Alhassan Ado Doguwa ya bayyana hakan ne cikin wata hira da suka yi da gidan Rediyon Jihar Kano a jiya Litinin.
Talla
Yace bayan gwamna Ganduje ya fadawa kowa laifin sa ya bukaci su yafi juna su manta da duk abun da ya faru a baya, domin samun nasarar jam’iyyar APC da ya takarar mu baki daya.
” Murtala ya bani hakuri kuma ni ma na bashi, ina kuma amfani da wannan damar duk wanda na batawa a wannan hatsaniya da ta faru ko dan APC ne ko ba dan jam’iyyar APC ba Ina mai bashi hakuri, abubuwan da akai min na jifa na da kwace motata duk na yafe domin na gamsu da yadda mai girma gwamna yayi mana sulhun”. Inji Doguwa
Alhassan Ado yace dama tun a ranar lahadi sai da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya kirawo shi saboda yaji labarin yana shirin ficewa daga APC ya bashi hakuri kuma yayi masa alkawarin za’a magance matsalolin domin jam’iyyar APC ta kafa gwamnati tun daga sama har kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...