Zargin ajiye kudi a gida: Gwamnatin kano tace zata ɗauki matakin Shari’a akan jaridar Sahara Reporters

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Gwamnatin Jihar Kano tayi martani game da wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Sahara Reporters ta wallafa, wadda ta bayyana cewa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana daga cikin gwamnoni uku da aka samu Maƙudan Ƙuɗaɗe a gidajensu.

 

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano kwamarade Muhammad Garba shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.

 

Muhammad Garba yace labarin bashi da tushe ballantana makama dan haka al’umma suyi watsi dashi.

 

Ya ƙara da cewa bayan sanarwa da hukumar EFCC ta fitar a kan wasu Gwamnoni 3 da tace tana sanya idanu akansu, bata bayyana sunan Gwamnonin ba.

Talla

To amma jaridar Sahara Reporters ta kama sunan Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda kuma hakan ya saba da ka’ida.

 

Muhammad Garba yace wajibine Jaridar ta Nemi yafiyar Ganduje bisa abinda ta wallafa wanda ba gaskiya bane, inda yace Idan basu nemi afuwar gwamnan ba to zasu dauki matakin Shari’a akan jaridar.

 

Muhd Garba yace gwamnatin jihar kano tana daga cikin jihohi kalilan da suke iya bisan albashi, Inda ya ko a lokacin da Sahara Reporters ta rubuta labarin tuni gwamnatin ta fara biyan ma’aikata albashinsu na watan October

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Za mu karasa Aikin tashar tireloli ta Dakatsalle, Gundutse da Ganduje ya yi watsi da su – Gwamnan Kano

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana...

Mun kawo takin zamani na 4tree fertilize don saukakawa manoma da rage tsadar abinchi a Nigeria

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa     A kokarinsu a ganin sun ragewa...

An sami cikas a shari’ar neman hana kananan hukumomin Kano kudadensu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Rashin halartar lauyan wanda ake kara...

Sharrin Zina: Shehu Tiktok ya Lashe Amansa

Daga Sidiya Abubakar   Shararren mai wasan barkwancin Nan na Tiktok...