Gwamna Kano ya kaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita 5 a garin Dawakin Tofa

Date:

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da aikin titi mai tsahon kilo mita 5 da fitilu a garin Dawakin Tofa, mahaifar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Aikin wanda sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya fara amma Ganduje ya gaza karasa shi tsahon shekaru takwas,amma yanzu gwamnatin Gwamna Yusuf ta kammala shi.

InShot 20250115 195118875
Talla

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, gwamna Yusuf ya jaddada cewa samar da fitulun tituna da ayyukan tituna na daga cikin Kudirin gwamnatinsa na samar da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar Kano.

Ya bukaci mazauna garin Dawakin Tofa da su yi amfani da sabbin kayayyakin da aka sanya a titin da kyau tare da sanya ido don kare su daga mabarnata.

Wani Dan Fansho a Kano ya sadaukar da kudin sallamarsa don gina masallacin Juma’a a garinsu

Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin, shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Hon. Anas Mukhtar Bello Danmaliki, wanda mataimakinsa Hon. Abdullahi Magaji Aliyu (Kosasshe) ya yabawa Gwamna Yusuf bisa kammala aikin da aka dade ana yi.

Ya bayyana yadda fitilun tituna suka kawo sauyi a yankin, yana mai cewa za su inganta tsaro, da inganta harkokin tattalin arziki, da inganta rayuwar al’umma a yankin.

Magaji ya kuma roki gwamnan da ya duba yiwuwar sake bude cibiyar kasuwanci a Dawakin Tofa wadda gwamnatin Ganduje ta rufe.

Ya jaddada cewa farfado da cibiyar zai baiwa matasan yankin damar samun sana’o’in dogaro da kai da bunkasar tattalin arzikin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related