Daga Sidiya Abubakar
Shararren mai wasan barkwancin Nan na Tiktok Muhd Shamsudden Adamu wato Shehun Tiktok ya karyata kansa bisa kagen zina da ya yiwa jarumar masana’antar Kannywood Umma Shehu.
” Mana da muka fada, kawai zama muka yi muka tsara, Amma ba gaskiya ba ne wallahi ban binciki ba, kawai na muka yi mata kage, Don Allah kiyi hakuri kuma duk wanda bidiyo na ya bata masa rai Ina ba shi hakuri”.

Shehun Tiktok ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tiktok.
Ya ce yana mai baiwa Jaruma Umma Shehu hakuri tare da neman afuwarta Kan kagen zina da ya yi mata, inda ya ce hakan ya zama izina a gare shi ba zai sake yin hakan ba ga umma Shehu ba har ga kowa ma.
Hukumar tace fina-finai ta haramtawa wani jarumi da wasu mata biyu Film da waka a Kano
Sannan Shehun Tiktok din ma yi bayanin cewa ba wani ne yasa suka yiwa jarumar kagen zina ba, kawai su suka shirya abun su kuma suka gabatar da kayansu ba tare da wani ya sa su ko ya sa su ba.
Idan za a iya tunawa tun a ranar asabar ake ta yan sanda suka kama Shehun Tiktok din bayan da ya saki bidiyon da yayi na kage ga jarumar Kannywood Umma Shehu.