Daga Ibrahim Sidi Mohammed Jega
Lahadi 06/11/2022
Sarkin kabin jega Alhaji Muhammad Arzika Bawa ya karbi bakuncin Sabon (Tafidan Jega) Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yiwa arzikin kasa zagon kasa EFCC. Alhaji Abdurrashid Yahaya Bawa jega.

Abdulrashid Bawa yaje masarautar ne domin yiwa Mai Martaba Sarkin godiya a bisa karramashi da masarautar ta yi na bashi Sarautar da mahaifinsa ya bari bayan da mahaifinsa ya samu sarautar Tafidan Gwandu.

Tun farko dai Abdulrashid Bawa jika ne ga Marigayi Alh. Yahaya Bawa jega, khalifan Shehu Balarabe mai goran faila, kuma shi ne Tafidan Gwnadu. shi kuma mahaifin Abdulrahid wato Alh. Ahmad Yahaya Bawa shi keda sarautar Tafidan Jega.
Bayan rasuwar Tafidan Gwandu sai mahaifinsa Alh. Ahmad Yahaya Bawa ya gaji babansa ya zama Khalifan Shehu Balarabe mai goran faila, daga bisani aka daga sarautarsa daga Tafidan jega zuwa Tafidan gwandu.

Sanin ya kamata da hangen nesa na Maimartaba sarkin kabin jega ya ga dacewa da kuma chanchantar baiwa Abdulrahid Bawa wanda yake Dah ne ga Tafidan Gwandu wannan sarauta ta Tafidan Jega.