EFCC ta fara bincike akan aikin samar da wutar Mambila – Ministan lantarki

Date:

Daga Maryam Abubakar Tukur

 

Kwamitin lura da harkokin wuta na Majalisar Dattawan Najeriya ya bayyana aikin gina madatsar ruwa ta samar da wutar lantarki na Mambila a matsayin fata kawai duk da biliyoyin naira da aka kashewa aikin.

 

Ministan wutar lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu shi ne ya bayyana haka duk da dimbin kudin da ake ware wa aikin a kasafin kudi na shekaera-shekara da ya kai biliyoyin naira.

 

Talla

Jaridar DailyTrust ce ta ruwaito hakan da cewa Ministan na fadar hakan ne yayin da kuma hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa, EFCC ke gudanar da bincike kan aikin.

 

Batun ya taso ne yayin zaman kare kasafin kudi na 2023 ranar Talata tare da Ministan wutar lantarki da sauran hukumomi da ke karkashin ma’aikatar.

 

Shugaban kwamitin Sanata Gabriel Suswam (PDP, Benue), ya ce abin takaici ne duk da dimbin kudin da aka yi ta ware wa aikin wanda tun shekara 30 baya aka tsara shi, ba abin da aka yi a aikin.

 

Sanatan ya ce tun 2017, ake ware wa aikin na Mambila kudi amma ba abin da aka yi duk da matsin lambar da Majalisun Dokoki da kuma ‘yan Najeriya suke yi.

 

Aikin madatsar ruwan wanda zai samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 3,050, idan aka kammala shi zai kasance mafi girma a Najeriya sannan kuma daya daga cikin mafiya girma a Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...