Sabon nau’in sauro mai sa zazzabi na kaura daga Asia zuwa Afirka

Date:

Daga Fa’iza Bala koki

Masana kimiyya sun ce wani mugun sauro da ke yada kwayar cutar da ke sa zazzabi, yana bazuwa zuwa Afirka daga Asiya, inda yake zama babbar barazana ga mazauna birni.

Wannan nau’in sauro wanda shi ne yake yada yawancin cutar maleriya da ake gani a biranen Indiya da Asiya, yana hayayyafa ne a cibiyoyin samar da ruwa na birane.
Kuma masanan sun ce wannan nau’i ne da kusan magungunan kashe sauro da ake amafani da su yanzu ba sa kashe shi.
Talla
BBC Hausa ta rawaito tuni wannan sauron ya sa an samu karuwar masu fama da cutar maleriya a Djibouti da Ethiopia, wanda hakan ya haifar da cikas ga yaki da cutar.
Masu bincike sun ce idan har ya ci gaba da yaduwa sosai a Afirka zai iya jefa rayuwar mutum miliyan 30 cikin hadari.
A nahiyar Afirka inda nan ne aka fi samun yawancin masu mutuwa a sanadiyyar cutar zazzabin sauro, galibi sauron da ke yada ta yana karkara ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...