Daga Nura Abubakar Cele
Mai Martaba Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar III ya umarci babban limamin Masarautar karaye ya yiwa dan takarar dan majalisar wakilai na kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso addu’o’in samun nasarar zaben dan majalisar wakilai.
An gudanar da addu’o’in ne lokacin da musa Iliyasu Kwankwaso ya ziyarci fadar Sarkin domin neman tubarrakin Sarkin kan takarar dan majalisar wakilai da yake yi a jam’iyyar APC.

Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso wanda shi ne Sarkin yaƙin Masarautar karaye yace ya ziyarci fadar Masarautar ne domin neman Sanya albarka sarkin kasancewar sa uban kasa Kuma Sarkin da karamar hukumar madobi take karkashin Masarautar sa.

” Babu shakka al’ummar karkara suna Jin dadin wadannan Sabbin Masarautun da gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya farfado da su, wanda hakan yake nuna cewa al’ummar wadannan yankuna ya zasu zabi jam’iyyar APC tun daga sama har kasa, saboda abun alkhairi da akai musu”. Inji Musa Iliyasu
Yace samar da Masarautun sun sa an Sami cigaba mara misaltuwa a kananan hukumomin da wadannan Masarautu suke, ta fuskar aiyukan raya kasa da cigaban al’umma da kuma Kara samar da aikin yi dama matso da mulki kusa da jama’a.

” Ina matukar farin ciki bisa yadda al’ummar yankin kura madobi da garun Mallam suka karbi takarar da nake yi, Kuma hakan ya nuna cikin ikon Allah zan lashe zaben, Kuma zamu tafi da kowa zamu taimaki har wadanda ba yan jam’iyyar mu ba, saboda dama halinmu kenan Kuma ba zamu chanza ba”. Inji Kwankwaso
Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma bada tabbacin nan gaba kadan zai ziyarci Masarautar Rano kasancewar kananan hukumomin kura da garun Mallam a karkashin Masarautar suke domin neman Sanya albarka a takarar sa daga mai Martaba sarkin Rano.