Rarara ya magantu kan batun rushe masa gida

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Shahararren mawakin Siyasar nan Dauda Kahutu Rarara yace yana da yaƙinin gwamnatin Kano ba za ta rusa masa gida ba, ko da kuwa a kan layin lantarki aka yi ginin, saboda kyakyawar alakar dake tsakanin shi da gwamnatin musamman Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

 

Rarara yace bai fi karfin doka tayi aiki a kansa ba, amma gwamnati ta bi doka wajen gina gidan.

 

 “Ina tare da Ganduje Kuma alakar mu tana nan,sai dai mun jima bamu hadu ba ko da yake dama mukan yi wata hudu zuwa shida bamu hadu ba, duk da dai na fahimci akwai munafukai da suke son lallai sai sun hadani da shi”. Inji Rarara

 

Rarara Dauda Kahutu ya musanya zargin da ake yi masa na cin zarafin Gwamnoni da zarar wa’adinsu ya zo karshe, yace mutane ba su fahimtar Hausar da yake yi a waka.

Talla

Rarara ya shaidawa DCL Hausa yana cikin wadanda suka amsa kiran Mai girma Muhammadu Buhari na yin sak, amma a karshe hakan ya kawo sakarkaru

 

A cewar Rarara, har yau yana tare da Abdullahi Ganduje sai dai idan gwamnan ya ja layi, yace amma akwai masu munafunci domin a hada shi fada da gwamnati.

 

A hirar, an ji mawakin yana cewa baya ga Murtala Garo, ya fi kowa shan wahala a tafiyar Ganduje, don haka ko an rusa masa gida, gwamna zai sake gina masa wani.

 

Mawakin yace a dalilin goyon bayan takarar Sha’aban Sharada a jam’iyyar adawa ta ADP, wasu suke ta zuga, suna so a tursasa shi ya yi jam’iyyar APC sak.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...