An baiwa hammata iska tsakanin Alhassan Ado Doguwa da Murtala Sule Garo 

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

Babban taron jam’iyyar APC da aka gudanar a Kano a ranar Litinin din da ta gabata ya rikide zuwa rikici, yayin da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alhassan Doguwa ya fadawa mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar Murtala Garo bakaken maganganu, kafin ya koma kan Murtala Garo.

Taron wanda aka gudanar a gidan mataimakin gwamna Nasir Gawuna, an shirya shi ne domin duba nasarori da kalubalen da aka samu a ziyarar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Alhassan Doguwa, wanda ba a gayyace shi wajen taron ba, ya je domin ganin shugaban jam’iyyar, Abdullahi Abbas.
Wata majiya ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewa, da isar shi wurin taron,  Doguwa ya fara korafin cewa shugabannin jam’iyyar sun mayar da shi saniyar ware kan al’amuran da suka shafi kudi, amma akan gayyace tare da sanya shi aiwatar da ayyuka masu wahala na jam’iyyar.
Talla
“Alhassan Doguwa ya fara afkawa mataimakin gwamnan ne da bakaken maganganu kafin ya juya ga Murtala Garo. Ya yi korafin cewa Murtala ya umarci yaransa da su rufe hotonsa da tutocin jam’iyyar yayin ziyarar Tinubu, alhali kuwa Murtala ba shi da masaniya a hakan,” inji wata majiya.
Majiyar Kadaura24 ta tattaro cewa Doguwa ya dauki kofin shayin dake gaban mataimakin gwamnan ya jefi Murtala Garo da shi,.
Wakilin majiyarmu ya tattaro cewa a kokarin da ya yi na tare kofin da hannunsa, sai fasashen kofin tangaran din ya raunata Murtala Sule Garo a hannunsa, abinda yasa Gawuna ya umarci Doguwa cewa ya fice masa daga gida, wanda hakan ne ya kawo ƙarshe taron .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...