Ilimi shi ne abun da ya kamata ‘yan siyasa su sanya a gaba a Nigeria – Sanata Kwankwaso

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana ilimi a matsayin mafi kyawun jari ga ‘yan siyasa.

 

Kwankwaso ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake gabatar da jawabinsa a wajen taron kololuwa karo na 3 da kungiyar Kwankwasiyya Development Foundation ta shirya domin bikin cikarsa shekaru 66 a Abuja.

 

A cewar Kwankwaso, Gidauniyar cigaban Kwankwasiyya ta yi imanin cewa mafi alherin abun da ya kamata Shugaban ya yiwa al’ummar sa shi ne ya samar musu da ilimi ba tare da la’akari da inda suka fito ba.

 

 

Ya ce sama da dalibai 3,000 ne suka ci gajiyar shirin bayar da tallafin karatu tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015 a lokacin yana gwamnan jihar Kano kuma dukkanin su ya’yan talakawan ne.

 

Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana cewa Ilimi ne yasa jiha kano ta buwaya a Arewacin Najeriya da Najeriya baki daya.

Talla

 Ya ce, “Mafi kyawun jari ga kowane dan siyasa shi ne ilimi. Babban ƙarfinmu a Kano, Arewacin Najeriya da Najeriya gabaɗaya shi ne ilimi.

 

“Kowa a kasar nan har da Fulanin suna so zuwa makaranta, batun matsalar kawai ita ce ba a ba su dama ba.

 

“Muna kuma bukatar mu horar da kuma da malamanmu, da kuma ba su duk abin da suke bukata,” in ji shi.

 

Kwankwaso ya ba da tabbacin cewa zai ci gaba da yi wa kowane dan Najeriya adalci ba tare da la’akari da addininsa ko kabila ba a matsayin wani bangare na manufofinsa na ganin Najeriya ta kasance ta kasa daya dunkulalliya.

 

Ya ce a kodayaushe yana sha’awar gudanar da shirye-shirye da ayyukan da za su yi tasiri ga rayuwar al’umma musamman ta fuskar ilimi.

 

Da yake magana game da shirye-shiryen ilimi na gidauniyar, Kwankwaso ya ce, “A koyaushe ina da burin ganin ya tallafawa al’umma musamman a fanin Ilimi.

 

“Mun fara aikin Gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation tun bayan zaben 2019. Ina mai farin cikin cewa a zaben 2019 a Kano ba mu da gwamna mai ci ko tsohon a kungiyarmu, ba wani minista mai ci ko tsohon ba mu da jakada ko wani mai mukami a gwamnatin tarayya ko jiha, amma sai dai wadannan matasa maza da mata a jihar Kano suka zabi dan takarar mu har muka lashe zaben gwamna da sauran su.

 

 

“Za mu ci gaba da yin duk abin da za mu iya a daidaiku da a kungiyance, a matsayinmu na ‘yan Kwankwasiyya da ’yan jam’iyyar NNPP da sauran masu hannu da shuni don ci gaban kasar nan,” inji shi.

 

Babban bako malami kuma shugaban Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Abuja, Mataimakin Farfesa Sherif Ghali, wanda ya gabatar da takarda mai taken “Jagora da kyakkyawan shugabanci a Najeriya: abun da Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi,” ya ce Najeriya na bukatar a samu shugaban kasa kamar Kwankwaso a 2023 wanda zai iya canza halin da ake ciki ya dora Najeriya a kan turba ta kowacce fuska.

 

Farfesa Ghali ya ce Kwankwaso ya mallaki abubuwan da ake bukata domin dawo da martabar Najeriya, da Kuma farfado da tattalin arziki don inganta Rayuwar su.

 

“Sanata Kwankwaso ya fahimci cewa za’a iya mulkin jama’a ba tare da la’akari da addininsu ba, kuma za ka yi musu adalci. Ya yi imani da rashin amfani da addini wajen gudanar da mulki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...