Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce ya bi ka’idojin da suka dace wajen sake fasalin wasu nau’ukan Naira guda uku.
Jami’in hulda da jami’a na babban bankin, Mista Osita Nwanisobi ne ya bayyana haka a lokacin da yake mayar da martani ga ministar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, wadda ta ce ba’a sanar da ma’aikatar ta ba.
Kadaura24 ta rawaito Nwanisobi ya bayyana mamakinsa da ikirarin na ministan, yana mai jaddada cewa CBN ya komai nasa bisa doka da oda.

Ya ce hukumar gudanarwar ta CBN bisa tanadin sashe na 2 (b) da sashe na 18 (a) da sashe na 19 (a) (b) na dokar CBN ta shekarar 2007, sun nemi amincewar shugaban kasa Muhammadu a rubuce Kuma Buhari ya amince da sake fasalin kuma takardun kudi na N200, N500, da N1,000.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su marawa aikin sake fasalin kudin kasar baya, inda ya ce hakan yana da amfani ga ‘yan Najeriya baki daya, yana mai kara jaddada cewa wasu mutane na tara makudan kudade a gidaje Maimakon a bankuna .
Wannan al’amari, a cewarsa, bai kamata duk wanda ke nufin alheri ga kasa ya kalubalence shi ba.
Don haka Nwanisobi ya bukaci ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da matsayinsu ba, da su goyi bayan aikin sake fasalin Naira, domin yana da amfani ga tattalin arzikin kasa