Daga Rukayya Abdullahi Maida
A kokarin sa Kara sada zumunci da Kuma zaburar da matasa Falakin Shinkafi Kuma Jarman matasan Arewa Amb. Dr. Yunusa Yusuf Hamza ya bada gudunmawar kayan kwallo domin su ji dadi yin wasanni.
Lokacin da ya ke mika kayan ga kungiyar kwallon kafa ta Super star Yakasai, Dr. Yunusa Yusuf ya yaba da yadda yan kungiyar suke gudanar da wasannin su cikin kwanciyar hankali da lumana.

” Na yi matukar gamsuwa da yadda kuke harkokin wasannin ku ba tare da fada da juna ba, hakan tasa naga dacewar na bada tawa gudunmawar don ku cigaba da sada zumunci da kuma motsa jiki yadda ya kamata”. Inji Jarman matasan Arewa
Dr. Yunusa Yusuf Hamza yace kamata yayi matasan wannan lokaci musamman masu harkar wasanni su rika zaman lafiya da juna musamman a lokacin wasa, saboda kwallon kafa tana sada zumunci sosai baya ga inganta lafiya da take yi.
” Ina fata wannan riguna da muka kawo muku zasu kara muku kwarin gwiwar cigaba da samun nasarar a wasannin da zaku buga a nan gaba, kuma zaku cigaba da ɗauko mana kofi a wasannin masu zuwa “. Inji Jarman matasan Arewa


Shugaban kungiyar kwallon kafan ta Super star Yakasai wanda ya karbi kayan a madadin ‘ya’yan kungiyar ya yabawa Amb. Dr. Yunusa Yusuf bisa tallafin kayan da ya basu, sannan sun bada tabbacin zasu Kara kaimi wajen samun nasarar a wasannin da zasu buga a nan gaba.
Ya ce kayan zasu Kara musu kaimi wajen cigaba da sada zumuncin da aka basu kayan domin su.