Duk da APC ce ke mulki zan kayar da Kabiru Gaya a zaben sanatan kano ta kudu – Kawu Sumaila

Date:

Daga Auwal Alhassan Kademi

 

Dan takarar Sanatan Kano ta Kudu a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP, Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila, a ranar Asabar, ya daki ƙirjin cewa zai kayar da Sanata Ibrahim Kabiru Gaya na jam’iyyar APC, duk da cewa jam’iyyarsa ce take kan mulki a Kano da kuma kasa.

 

Kabiru Gaya ya sake tsayawa takarar neman wakilcin Kano ta Kudu a majalisar dattawa karo na hudu a karkashin jam’iyyar APC, sai dai Kawu Sumaila ya ce al’ummar Kano ta Kudu na neman samun wakilci nagari, inda ya ba da misalin yadda al’ummar yankin suka karbi takarar sa musamman Saboda yadda suka halarci yakin neman zabensa a Sumaila kwanakin baya.

 

Kawu Sumaila, wanda shi ne ya kafa Jami’ar Al-Istiqama da ke garin Sumaila a Kano, kuma ya wakilci mazabar Takai/Sumaila a Majalisar Wakilai a tsakanin 2003 zuwa 2015.

 

Talla

Ya na daga cikin ‘yan siyasar da suka bar jam’iyyar APC zuwa NNPP, gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar a Kano saboda abin da ya bayyana a matsayin yunkurin rashin adalci da jam’iyyar take shirin yi masa.

 

Tsohon babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar wakilai ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da yan jaridu, wanda kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta correspondent chapel ta shirya a otel din Grand Central dake Kano.

 

A cewarsa, “A Kano karfin mulki ba ya tasiri… Yanzu a Kano ta kudu gani Kawu Sumaila, ga dan takarar mu na gwamna na jam’iyyar NNPP Abba Yusuf, ga kuma ubangayya babban kwamandan mu kuma dan takarar shugaban kasa, Dakta Rabi. ‘U Musa Kwankwaso ta yaya, Kabiru Gaya da sauran ‘yan takarar APC za su yi wani tasiri.

 

 

 “Ba za su iya kayar da mu a Kano ba, a Kano ta Kudu mutane sun gaji da su, ba ka ga abin da ya faru ba, a lokacin da na kaddamar da yakin neman zabe ba, ba ka ga yadda jama’a suka fito ba…” Inji Kawu Sumaila

 

Kawu Sumaila, ya ce idan aka zabe shi a matsayin Sanata, falsafar siyasarsa za ta kasance a kan tsarin adalci na zamantakewa tare da sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya dora mana.

 

“Ilimi na daga cikin abun da zamu fi baiwa fifiko saboda shi ne babban jigo a jam’iyyar NNPP Kuma mun ga yadda bada ilimi ga al’umma ta yi tasiri ga rayuwar al’umma, hakan tasa na kafa jami’a ta ta al-istiqama don haka zamu dora idan muka sami dama”.

 

Zan tabbatar da an samu adalcin wajen rabon arzikin kasa, a nan Kano zan tabbatar da akwai wata kungiya mai karfi ta tuntuba a karkashina wadda za ta aiwatar da muradun mu da kuma tabbatar da cewa mun samu kaso mai tsoka na dimokuradiyya daga tarayya”.

 

Kawu Sumaila ya kuma nuna damuwa kan yadda tashe-tashen hankula ke kara kamari a yankin Kudu maso Gabas da wasu yankunan Arewa sakamakon rashin adalci a cikin al’umma, inda ya tabbatar da cewa idan ya zama Sanata zai tabbatar da an samar da Adalci ga kowa ba tare da la’akari da bambamcin kabila da addini ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...