Al’ummar Tukuntawa sun godewa Ganduje saboda basu filaye kyauta a gidan Radio manoma

Date:

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa

Al’ummar unguwar Tukuntawa dake karamar hukumar birni sun yabawa gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje sakamakon wasu filaye da gwamnan ya baiwa al’ummar unguwar cikin rukunin filayen da aka yanka a gidan radio manoma.

Taron dai an shirya taron ne bisa jagorancin mai unguwar Malam Nuhu Garba.
Talla
 Yayin taron Malam Nuhu Garba ya ce ya zama dole su shirya taron godiya Saboda karamcin da gwamna Ganduje yayi musu, wanda ba lallai idan wani gwamnan ne yayi musu haka ba.
Yace filayen zasu taimakawa al’ummar yankin baki daya wajen inganta Ilimi da tsaron su dama tabbatar fa cewa gwamnatin bata manta da al’ummar yankin ba.

“Cikin filayen da gwamnatin ta bamu Akwai wanda Zamu Gina makarantar sakandire da Kuma wanda za’a Gina ofishin yan sanda da na asibitin da Kuma wanda za’a mayar da shi makabarta wadda nan ne gidan kowa na ƙarshe”. Inji Malam Nuhu Garba

Talla
A madadin al’ummar Unguwar Malam Nuhu Garba godewa MD na KNUPDA ACt. Sulaiman Abdulwahab bisa tabbatarwa da al’ummar Unguwar kason nasu filayen domin su gudanar da abubuwan da zasu taimaki yan unguwar.
Daga karsheya hori al’ummar Unguwar da suyi duk mai yiyuwa wajen ganin sun alkinta tare da Sanya Ido a guraren da gwamnatin ta basu, don gudun kada bata gari su Maida wajen wurin aikata laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu Yanzu: Hukumar KNUPDA ta rushe gaban shagon jarumar Tiktok Rahama

Daga Rahama Umar Kwaru   Hukumar KNUPDA ta kaddamar da rushe...

Wata kungiya ta bukaci Gwamnan Kano ya dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Wata kungiya mai zaman kanta mai...

Kwankwaso ba zai koma APC ba – Buba Galadima

Kusa a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya karyata jita-jitar...

Yadda gwamnan Kano ya ke rabon kujerun aikin hajjin bana kamar gyada

Daga Rahama Umar Kwaru Al'ummar jihar Kano na cigaba da...