Daga Rukayya Abdullahi Maida
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri yayin da ake kokarin shawo kan matsalar karancin man da ake fama da shi a halin yanzu sakamakon ambaliyar ruwa da ta kai ga lalata wasu manyan tituna a wasu sassan jihohin Arewacin kasar nan.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban kungiyar IPMAN reshen Arewacin Najeriya, Alhaji Bashir Danmalam ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Asabar.
Shugaban IPMAN ya bayyana cewa ana sa ran motoci kusan 200 dake dauke da man fetur daga Calabar ana sa ran su isa Abuja da sauran sassan jihohin Arewa domin rabawa gidajen mai.
Ya ce ana sa ran motocin za su bi ta Ikom, Ogoja, Katsina Ala, Vandeikia har zuwa Lafiya zuwa Abuja.
Danmalam ya yabawa Manajan Daraktan Kamfanin (PPMC), Alhaji Isyaku Abdullahi bisa alkawarin tallafa wa ‘yan kasuwar da man dizal domin rage musu wahalhalun da suke fuskanta sakamakon tsadar dizal din .
Ya ce kamfanin sarrrafa albarkatun mai na NNPC tare da hadin gwiwar IPMAN na kokarin ganin an samar da isassun mai da kuma rarraba shi, inda ya ce nan ba da dadewa ba za a kawo karshen karancin man fetur din .
Ya kuma bayyana cewa, kamfanin na NNPC ya kuma tattara jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa domin su taimaka wajen kawar da tsinkoso a hanyoyin da abin ya shafa domin jigilar kayayyaki cikin sauki zuwa sassan Arewacin kasar nan.
Bugu da kari, ya ce kamfanin na NNPC ya umurci kamfanin CCC na yan kasar China da ke aikin hanyoyin da abin ya shafa su koma wuraren da suka lalace domin su.