Gwamnatin tarayya na neman gwamnoni su saki kaso 30 na fursunoni a jihohinsu

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

 

Gwamnatin tarayya Nigeria ta ce tana shirin ganawa da gwamnonin jihohi na ƙasar nan don cimma matsaya kan sakin aƙalla kashi 30 cikin 100 na fursunoni daga gidajen yarin da ake tsare da su a faɗin ƙasar.

 

Minustan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan lokacin da yake magana yayin wani taron ƙara wa juna sani da kamfanin labarai na kasa, NAN, ya shirya a Abuja.

 

Ministan ya ce yunƙurin ya zama dole saboda kashi 90 cikin 100 na mutanen, ana tsare da su ne sakamakon karya dokoki daban-daban na jihohin.

Talla

Haka nan, ya ce fiye da kashi 70 cikin 100 na fursunoni 75,635 da ake tsare da su yanzu haka jiran shari’a suke yi.

 

Ƙasa da kashi 10 cikin 100 ne kawai na fursunonin suka karya dokar gwamnatin tarayya, a cewar ministan.

 

“Rage cunkoso a gidajen yari 253 a faɗin Najeriya ya zama dole saboda bai kamata wasu daga cikin fursunonin su ci gaba da zama a gidan yari ba,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Dokokin Kano ta yi Doka kan masu tufar da yawu da majina a titi

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin...

Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau...

Kamfanin Gerawa ya ba da tallafin Kwamfutoci 100 ga al’ummar Gezawa

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kamfanin shinkafa na Gerawa Rice Mills...

Gwamnan Kano ya baiwa maja-baƙin Sheikh Karibullah da wasu malamai muƙami

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...