Daga Aleeyu Abdullahi Danbala Gwarzo
Al’ummar garuruwan Rafawa da Dogami da Munawa da lahadin kara da dogami da tudunkudi da sauran kauyikan da suke kusa da yankin a karamar hukumar Gwarzo sun ce zasu kauracewa zaben shekara ta 2023 saboda rashi yi musu hanyar data hade garuruwansu.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban kungiyar cigaban garuruwan Ahmad Musa Siri ne ya bayyana hakan yayin da suka gudanar da taron neman hadin kan al’umma yankin.
“Matukar mahukunta ba su zo sunyi mana aikin hanyar nan ba kafin zabe to muna shida musu cewa kada ma a kawo mana akwatunan zabe domin babu Wanda zai fito don ya kada kuri’a zaben banana wannan ita ce matsayarmu” . A cewar Musa siri
Ya kara da cewa al’ummar dake yankin suna shan bakar wahala sosai wajen fitar da marasa lafiya zuwa asibiti, saboda saboda basu da asibiti a yankin sai sun fito cikin garin Gwarzo, a wani lokaci marasa lafiya kan rasa ryukansu kafin a karaso zuwa Gwarzo a dalilin lalacewar hanyar.
“Alhamdulillah mun sami goyon bayan dukkanin al’ummar mu Kuma muddin gwamnati bata zo ta gyara mana hanyar mu ba, to baza mu yi zaben shekara ta 2023 wannan ita ce matsayarmu.” Inji Musa Siri
Daga karshe Shugaban kungiyar yayi kira ga mahukunta dasu dubi halin da al’ummar su suke ciki ayi musu wannan hanyar ko dan a inganta Rayuwar su.